• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DUBUN TURJI NA GAB DA CIKA-GWAMNA TAMBUWAL

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya ce dubun babban barawon dajin nan na jihar Bello Turji na gab da cika.
Gwamnan na magana ne a taron jama’a bayan ‘yan bindiga sun yi kisan gilla ga wani dan kasuwa a yankin karamar hukumar Sabon Birni.
‘Yan bindigar dai sun shiga kauyen Kurawa a Sabon Birni inda su ka yi kisan gilla a kan dan kasuwar mai suna Bello Yellow kazalika su ka sace mutum 5.
Babban abun takaicin cikin mutum 5 din 2 matan aure ne inda uku maza ne.
Gwamna Tambuwal ya yi taro da jama’ar yankin da rashin tsaron ya ta’azzara ne don baiyana mu su irin tsayin dakan gwamnati don gamawa da miyagun irin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *