• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DUBBAN MASU ZANGA-ZANGAR NEMAN ADALCI GA PALASDINAWA SUN CIKA TITUNAN BIRANEN AMURKA

Dubban masu zanga-zangar neman a yi wa Palasdinawa adalci bayan ruwan wuta da Isra’ila ta shafe kwana 11 ta na yi a Gaza; sun yi dafifi a titunan buranen Amurka su na daga tutar Palasdinawa.

An gudanar da babbar zanga-zangar a dandalin tunawa da LINCOLN a birnin Washington DC.

Hakanan an yi zanga-zanga a wasu wajeje 15 ciki da jihar Iowa, Illinois, California da Texas.

Masu zanga-zangar na nuna lokaci ya yi da za a ba wa Palasdinawa ‘yancin su ta hanyar wargaza mamaya, mulkin mallaka, nuna bambancin jinsi da kisan kare dangi daga yahudawan Isra’ila.

Hakanan masu zanga-zangar na bukatar gwamnatin Amurka ta azawa Isra’ila takunkumi don laifukan yaki da ta aikata.

A yakin na kwana 11, sojojin Isra’ila sun yi amfani da jiragen yaki 160 da sauke boma-bomai masu nauyin ton 80.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.