• Sun. Nov 28th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DSS TA CAFKE WASU AMURKAWA 2 DA DAN FARANSA DON DAUKAR BIDIYON ‘YAN AWARE BA IZINI

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya DSS ta cafke Amurkawa biyu ‘yan asalin Isra’ila da Bafanshe daya na daukar faifan bidiyon farafagandar ‘yan Biyafara ba tare da izini ba.

Lamarin kamar yanda The Will ta ruwaito ya auku ne a jihar Anambra inda mutanen uku ke daukar faifan bidiyo don taimakawa yada msnufofin ‘yan awaren.

Mutanen sun hada sa Rochman Rudy, Leibman Abdrew da Benaym Edouard David.

Labarin dai ya nuna an garzaya da mutanen Abuja inda a ke tsare da su duk da cewa David ba shi da lafiya don haka a ka damka shi ga ofishin jakadancin Faransa da za ta rika kawo shi a duk lokacin da a ke bukatar sa.

Madugun ‘yan awaren Nnamdi Kano na hannun ‘yan DSS bayan kamo shi daga gabashin Afurka.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *