• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DONALD TRUMP YA KAMU DA CORONA

Shugaban Amurka Donald Trump ya baiyana cewa ya kamu da cutar korona bairos da hakan ma ya kama matar sa Melania. kamuwar Trump da cutar ta zo ne sa’o’i bayan tabbatar da kamuwar babban hadimar sa Hope Hicks wanda su ka kasance tare a tafiye-tafiye da dama. 

Ba a dai baiyana cewa ko Hicks ne ya harbi Trump da cutar ba. Trump da Melania sun killace kan su na tsawon lokacin da za a tabbatar sun warke daga cutar.

Fiye da mutum dubu 200 su ka mutu sakamakon annobar a Amurka. Trump na fuskantar Neman tazarce a zaben kasar da za a gudanar ranar 3 ga watan nuwamba inda zai kara da tsohon mataimakin shugaban kasar Joe Biden.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “DONALD TRUMP YA KAMU DA CORONA”
  1. My partner and I stumbled over here coming from a different website and thought I should check things out.
    I like what I see so now i am following you.
    Look forward to exploring your web page repeatedly.

Leave a Reply

Your email address will not be published.