• Sun. Dec 5th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DONALD TRUMP NA SHIRIN KAI KARAR TIWITA, FESBUK DA GUGUL

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya shigar da karar kamfanonin sadarwar yanar gizo don yanda ya ce sun hana shi dama ba bisa ka’ida ba.

Kamfanonin sun hada da Tiwita, Fesbuk da Gugul.

Trump a zantawar sa da manema labaru a New Jersey Amurka, ya ce zai zama ja gaba a  karar ba kawai ga kamfanonin ba har da shugabannin su Mark Zuckergerg, Sundar Pichai da Jack Dosey.

Tsohon shugaban ya ce ya na son karar ta kawo karshen hana shi dama da sanya shi a bakin littafi da kamfanonin su ka yi.

An shigar da karar a kotun Florida.

In za a tuna gabanin babban zaben Amurka, kamfanin tiwita ya dakatar da shafin Donald Trump inda su ma sauran kamfanonin su ka bi sahu.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *