• Tue. Oct 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DOLE TIKITIN PDP YA KOMA KUDU A 2023-BODE GEORGE

 

Tsohon mataimakin shugaban PDP na kudu Chief Bode George ya ce ya zama wajibi tikitin shugaban kasa na jam’iyyar ya koma kudu a 2023.

George a sanarwar da ya fitar ya nuna barin dama a bude (ba tare da ware bangaren da zai yi takara ba) na da hatsari ga jam’iyyar.

Bode George wanda kotu ta taba daurewa saboda samun sa da cin hanci da rashawa, ya ce iyayen jam’iyyar sun tsara yanda mulkin karba-karba na manyan mukamai zai zama tsakanin shiyoyin siyasar Najeriya 6.

Mukaman sun hada da na shugaban kasa, mataimakin sa, shugaban majalisar dattawa, kakakin majalisar wakilai, sakataren gwamnati da kuma shugaban jam’iyya.

George ya ce tun da jam’iyyar ta amince da tura mukamin shugabancin ta arewa to tikitin shugaban kasa zai koma kudu.

Wannan ya kara nuna rashin jituwa a cikin jam’iyyar PDP inda bangaranci da muradun son tsayawa takara ke neman jefa jam’iyyar a sabuwar rigima.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
3 thoughts on “DOLE TIKITIN PDP YA KOMA KUDU A 2023-BODE GEORGE”
  1. I am really impressed with your writing skills and also with
    the layout on your blog. Is this a paid theme or did
    you customize it yourself? Either way keep up the nice
    quality writing, it’s rare to see a nice blog like this one nowadays.

  2. You really make it seem so easy with your presentation but I find this topic to be actually something that I think I would never understand. It seems too complicated and very broad for me. I am looking forward for your next post, I抣l try to get the hang of it!

  3. Greetings! I know this is kind of off topic but I was wondering which blog platform are you using for this site? I’m getting sick and tired of WordPress because I’ve had problems with hackers and I’m looking at alternatives for another platform. I would be awesome if you could point me in the direction of a good platform.

Leave a Reply

Your email address will not be published.