• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DOLE KOWA YA DAGE DON HANA NAJERIYA AUKAWA BABBAR FITINA-BARISTA MUSTAPHA

Jigon APC Braista Bello Mustapha ya bukaci shugabannin kare muradun sassan Najeriya su yi tsayin daka ga bayanan hadin kan kasa don kare Najeriya daga aukawa fitinar da ba a san karshen ta ba.

Barista Bello Mustapha na magana kan kungiyar tuntubar juna ta arewa ACF, kungiyar kare muradun yarbawa Afenifere da ta kabilar Igbo Ohaneze Ndigbo.

Barista Mustapha ya ce ya zama wajibi matasa su kare Najeriya matukar su na son zama shugabanni a gobe.

Barista Mustapha wanda ya ce shugaba Buhari na iya bakin kokarin sa wajen inganta lamuran tsaro, ya bykaci matasa su hada kai wajen kare dimokradiyya mai tsabta don cin gajiyar ta a nan gaba kadan.

Hakanan masanin shari’ar ya bukaci APC ta zabi matashi a matsayin sabon shugaban jam’iyya don hakan ya zama hanyar shiga babban zabe na 2023 da kwarin guiwa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.