• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DOKAR HANA YAWON DARE A KARU JIHAR NASARAWA TA FARA ZAFI INDA MUTANE KAN SHIGE GIDAJEN SU ALA TILAS

Dokar hana yawon dare a yankin karamar hukumar Karu da ke Nasarawa daf da Abuja ta fara zafi inda mutane kan yi kokarin shigewa gida don gudun cin karo da jami’an tsaro.

Tun ranar talata shugaban karamar hukumar Mr.Jmaes Thomas ya aiyana dokar da za ta fara aiki daga karfe 10 na dare zuwa 6 na safe.

Mr.Thomas ya ce an dau matakin ne don karfafa don yanda ‘yan ta’adda kan yi yunkurin sulalowa don fakewa a yankin kasancewar sa ya na makwabtaka da Abuja.

An samu rahoton wadanda wa imma ba su san zafin dokar ba ko ma ba su ankara ba sun gamu da fushin jami’an tsaro.

Dama jami’an soja sun kafa wani gagarumin shingen binciken motoci kan hanyar Abuja da jihar Nasarawa inda hakan kan kawo cunkoson motoci mai tsananin gaske

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.