• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DIMOKRADIYYAR NAJERIYA NA ZAMA TA ‘YAN JARI HUJJA

ByNasiru Adamu El-hikaya

Apr 25, 2022

Masu sharhi kan lamuran yau da kullum a Najeriya na nuna dimokradiyyar Najeriya na komawa hannun ‘yan jari hujja.
Ra’ayoyin jama’a sun nuna takaicin yanda sai masu hannu da shuni ko wadanda ‘yan jari hujja su ka dau nauyin su ke iya fitowa takarsr mukamai.
Kalubalen ya shafi manysn jam’iyyu ne da ke da tagomashin lashe zabe saboda karfin aljihu, wakilai a birane da kauyuka da kuma mallakar masu logar samar da kuri’a.
Kananan jam’iyyu kan zama dama ta mara baya ne ga manyan jam’iyyu don da zarar wani dan takara ya fito a karamar jam’iyya sai ka ji an ce ayya ba zai kai labari ba.
Duk ma abun da ya tsokano doguwar muhawarar nan shi ne tsadar neman tikitin takara a jam’iyyar APC da ta tallata kan ta da cewa ta talakawa ce.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “DIMOKRADIYYAR NAJERIYA NA ZAMA TA ‘YAN JARI HUJJA”
  1. Good day! I could have sworn I’ve been to this blog before but after reading through some of the post I realized it’s new to me. Nonetheless, I’m definitely happy I found it and I’ll be bookmarking and checking back frequently!

Leave a Reply

Your email address will not be published.