• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DIMOKRADIYYA: DAWO DA ZABEN FIDDA GWANI HANNUN HUKUMAR ZABE NE MAFITA – KABIRU ADAMU

A cigaba da sharhi kan dimomradiyyar Najeriya, ma’abota lamuran zabe da siyasa na cewa dawo da hakkin gudanar da zaben fidda gwani hannun hukumar zabe ne zai gyara harkar dimokradiyya.

Wannan dai a sharhin masanan, zai ba da dama mutanen da ke da goyon bayan jama’a ba jami’an jam’iyya ba za su samu damar yin takara da lashe zabe.

Kamar yanda a ke kira ga mika gudanar da zaben kananan hukumomi ga hukumar zabe ta kasa INEC, haka ma batun zaben fidda gwani ya zama muhimmin batu don yanda takaddamar da ke sa kotuna rushe zabe bayan wasu sun lashe kamar yanda ya faru a Zamfara inda Shehu Mukhtar Kogunan Gusau ya rasa kujerar gwamna, hakanan Celestine Omehia ya bar fadar gwamnatin Ribas a ka rantsar da tsohon gwamna Rotimi Amaechi. A Bayelsa Douye Diri na PDP ya tsinci dami a kala bayan kotu ta hana rantsar da David Lyon na APC. Ga ma Hope Uzodinma ya zama gwamna a Imo duk da shi ya zo na hudu a yawan kuri’u ya sa dole Emeka Ihedioha ya kwashe kayan sa daga fadar gwamnati a Owerri.

Tsohon darakta a hukumar zabe sarkin tafarkin Bauchi Kabiru Adamu ya ce amshe ikon zaben fidda gwanin ‘yan takarar jam’iyyu zai kawo maslaha.

Ita kuma malamar jami’a a Itas Gadau Dr.Furera Bagel na nuna tamkar a na gaggawa ne wajen gwada dimokradiyyar Najeriya da kasashen duniya da su ka dade a cikin ta.

Babban zaben Najeriya na zuwa a 2023, inda shugaba Buhari ke fatar APC tazarce don manufofi irin na gwamnatin sa su dore, yayin da babbar jam’iyyar adawa ta PDP ke arar logar kamfen din Bubari wato “Jiki Magayi.”

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “DIMOKRADIYYA: DAWO DA ZABEN FIDDA GWANI HANNUN HUKUMAR ZABE NE MAFITA – KABIRU ADAMU”

Leave a Reply

Your email address will not be published.