• Tue. Oct 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DIG JOSEPH EGBUNIKE NE ZAI KULA DA TSARO A ZABEN JIHAR ANAMBRA

ByYusuf Yau

Oct 27, 2021
Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Usman Baba Alkali ya tura DIG Joseph Egbunike don kula da lamuran tsaro a zaben gwamnan jihar Anambra.
 
Za a gudanar da zaben a ranar 6 ga watan gobe.
Barazanar ‘yan awaren Biyafara ta kawo cikas a zaben ya sa rundunar ‘yan sandan daukar gagarumin matakin tsaro da ya hada da tura mataimakan kwamishinan ‘yan sanda wato ACPs.
 
Rundunar ba ta bar DIG Egbunike shi kadai ba, ta kara ma sa mukaddashin babban sufeto mai kula da aiyuka DIG Zaki Ahmed don taimaka ma sa tabbatar da gudanar da zaben lami lafiya.
 
Yanda yawan manyan jami’an ‘yan sanda ya ke ga zaben an tura mataimakan babban sufeto 5, kwamishinoni 14, mukaddasan kwamishina 31 da mataimakan kwamishina 21.
Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.