• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DEBORA-SHUGABA BUHARI BAI GOYI BAYAN ABUN DA YA ZAIYANA DA DAUKAR DOKA A HANNU BA

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna takaicin yanda ‘yan makarantar kolejin ilimi ta Shehu Shagari a Sokoto su ka kashe daliba Debora Samuel wacce ta aibanta Manzon Allah ba tare da barin a damka ta ga hukuma ba.

A sanarwa daga mai taimakawa shugaban kan labaru Garba Shehu, shugaba Buhari ya ce daukar doka a hannu ba zai kawo zaman lafiya ba ko biyan bukatar jama’a ba.

Shugaban ya ce musulmi sun yi amanna da mutunta dukkan Annabawa cikin da Annabi Isa da ke matsayin Yesu ( a wajen addinin kirista)

Shugaban ya ce sam ba a amince a Najeriya mutane su dau doka a hannu ba.

Yayin da shugaban ke jan kunnen mutane su iya bakin su wajen furta ra’ayi da zai iya kawo tashin hankali, ya yabawa matakan gaggawa da gwamnati ta dauka don dakatar da fitinar.

Malamai a masallatan jumma’a daban-daban sun yi tir da duk wani yanayi da zai sa wani ya aibanta Manzon Allah, inda su ka bukaci jama’a su hada kai da hukuma a wajen magance irin wannan akasin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “DEBORA-SHUGABA BUHARI BAI GOYI BAYAN ABUN DA YA ZAIYANA DA DAUKAR DOKA A HANNU BA”
  1. Hmm it looks like your website ate my first comment (it was super long) so I guess I’ll just sum it up
    what I wrote and say, I’m thoroughly enjoying your blog.
    I as well am an aspiring blog blogger but I’m still new to the whole thing.
    Do you have any tips for first-time blog writers?
    I’d genuinely appreciate it.

Leave a Reply

Your email address will not be published.