• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DCP ABBA KYARI YA SAUKA A MAKURDI DON BINCIKEN LABARIN YUNKURIN KASHE OTOM

ByNasiru Adamu El-hikaya

Mar 29, 2021

Jami’in bincike na musamman na rundunar ‘yan sandan Najeriya Abba Kyari ya sauka da tawagar sa Makurdi babban birnin jihar Binuwai don bincike kan labarin da gwamnan jihar Samuel Otom ya bayar cewa ‘yan miyetti Allah sun yi yunkurin kashe shi.

Babban sufeton ‘yan sanda Muhammadu Adamu ya tura tawagar inda za ra karbi duk aikin binciken wannan hari da a ka ba da labari an kai.

Tawagar za ta gano da kuma kamo duk wadanda su ke da hanny a kai harin don fuskantar shari’a.

A na sa ran tasagar ta Abba Kyari za ta aiki da jami’an rundunar ‘yan sanda a jihar Binuwai da sauran jama’a don samun nasarar aikin binciken.

In za a tuna duk Miyetti Allah guda biyu sun yi watsi da kai hari kan gwamna Otom sy na masu cewa labari kawai ta shirya marar tushe.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *