Daya daga manyan dattawan arewacin Najeriya Alhaji Ahmed Joda ya riga mu gidan gaskiya.
Marigayin dai tsohon babban sakatare ne a matakin taraiya.
Alhaji Joda ya rasu a Yola helkwatar jihar Adamawa ya na mai shekaru 91.
Marigayin ne ya jagoranci kwamitin tsara bayanai na karbar mulki na shugaba Buhari.
A littafin tarihin aiki da tsohon shugaba Olusegun Obasanjo ya rubuta, ya yabawa Alhaji Joda don yanda ya taimaka ma sa lokacin da a ka kai shi gidan yarin Yola a zamanin marigayi Janar Sani Abacha.
Obasanjo ya ce dan arewa ne ya daure shi amma wani dan arewan ne ya yi zaman gidan yarin; bisa ma’ana don Baba Joda na zuwa ya wuni a wajen sa ya na debe ma sa takaici.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀