Daular Larabawa ta yanke matsayar dawo da ba da izinin shiga kasar ga ‘yan Najeriya da tun farko ta dakatar saboda tsoron ta’azzarar cutar korona.
Sai da ta kai ga Najeriya ta haramtawa jirgin Daular Larabawan “EMIRATES” shigowa Najeriya don matakin in-ka-yi-min na-yi-ma ka.
‘Yan Najeriya dai kan shiga Daular Larabawa don kasauwanci, yawon hutawa ko neman magani inda wasu kan tura ‘ya’yan su, su yi karatu.
Har yanzu Najeriya na kan bakan ta na hana jiragen kasashen da duk su ka hana ‘yan Najeriya shiga kasashen su.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀