• Thu. Dec 9th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DAULAR LARABAWA TA SAKE JANYE DAMAR SHIGA KASAR TA DAGA NAJERIYA

ByYusuf Yau

Jun 22, 2021 , ,

Daular Larabawa ta sake janye damar shiga kasar ta kasa da sa’a 48 bayan dawo da damar ga Najeriya.

Lamarin dai ya ba da mamaki don sake rufe damar har illa Masha Allahu wanda dama an yi ne kan barazanar cutar korona.

Daular Larabawa ta janye batun dawo da saukar jiragen ta EMIRATES a Lagos da Abuja  har sai ta sake nasartar lamura.

Hakanan kasar ta Dubai ta ce ba za a bari duk wani fasinja da ya biyo ta Najeriya a mako biyu da su ka wuce ya shiga Daular Larabawa ba.

Duk da haka Daular ta nuna cewa ta na tare da Najeriya kuma za ta dawo da hada-hada tsakanin kasashen biyu.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *