• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DAULAR LARABAWA DA BAHRAIN SUN SANYA HANNU DON DAWO DA CIKAKKIYAR HULDA DA ISRA’ILA A TARO GABAN DONALD TRUMP A FADAR WHITE HOUSE

Shugaban Amurka Donald Trump ya karbi bakuncin wakilai daga Daular Larabawa da Bahrain a fadar White House inda su ka rantaba hannun zaman lafiya da kawance da Isra’ila. Yarjejeniyar mai taken “SULHUN IBRAHIM” ta samu halartar ministan wajen Daular Larabarawa Sheikh Abdullah Bin Zayed, ministan wajen Bahrain Abdullatif Bin Rashid Al-Zayani da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu. Baya ga Masar da Jodan, Daular Larabawa da Bahrain ne zuwa yanzu a hukumance su ka kulla kawance da Yahudawa. Duk da Palasdinawa na takaicin lamarin, masu yarjejeniyar na cewa su na fatan sulhun ya zama sanadiyyar kafa kasar Palasdinawa a gefen ta Yahudawa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “DAULAR LARABAWA DA BAHRAIN SUN SANYA HANNU DON DAWO DA CIKAKKIYAR HULDA DA ISRA’ILA A TARO GABAN DONALD TRUMP A FADAR WHITE HOUSE”
  1. Thanks for a marvelous posting! I truly enjoyed reading it, you are a great author.
    I will ensure that I bookmark your blog and will often come back later on. I
    want to encourage that you continue your great
    work, have a nice evening!

  2. My family members all the time say that I am killing my time here at web, however I know I am getting experience everyday
    by reading such pleasant content.

Leave a Reply

Your email address will not be published.