Yawan dauke wutar lantarki ya zama babban abun damuwa a babban birnin Najeriya Abuja.
A kan dauke wutar tsawon wuni ko a kwana ba wutar amma sai a dawo da ita na dan kankanin lokaci a sake daukewa.
Dauke wutar na shafar hatta anguwannin masu hannu da shuni na zagayen fadar Aso Rock.
Kazalika tsadar iskar gas ya sa masu manyan na’urorin janareta ba sa iya kunna na’urorin.
Bayanan da a ke samu na nuna karancin wutar daga cibiyoyin samar da wutar.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀