• Fri. Dec 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari...

DARURUWAN MASU ZANGA-ZANGA SUN FITO A BIRNIN TUNIS DON TUNA CIKAR SHEKARU 11 DA JUYIN JUYA HALI

ByNoblen

Dec 18, 2021 ,

Daruruwan mutane sun baiyana kan tituna a babban birnin kasar Tunusiya wato Tunis daidai cikar shekaru 11 da juyin juya hali a kasar ta larabawan Afurka ta arewa.
Mutanen na rike da kwalaye da zargin kwace mulki kacokan da shugaban kasar Kais Saeid ya yi ta hanyar korar majalisar zartarwa da majalisar dokoki.
Matakin na Kais Saeid tun farko ya samu yabo don hakan hanya ce ta maganin ‘yan jari hujja da su yi babakere a madafun iko da karya tattalin arzkin kasar.
Duk da haka akwai wadanda a cikin zanga-zangar ke mara baya ga shugaban.
A 2010 wani matashi mai sayar da jarida Muhammad Bouazizi ya cinnawa kan sa wuta ya kone, da hakan ya haddasa zanga-zangar mako 4 da ya sanya fatattakar tsohon shugaban kasar Zainul Abidin bin Ali daga mulki.

KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “DARURUWAN MASU ZANGA-ZANGA SUN FITO A BIRNIN TUNIS DON TUNA CIKAR SHEKARU 11 DA JUYIN JUYA HALI”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *