Dan tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido ya samu tikitin takarar gwamnan jihar ta Jigawa a inuwar jam’iyyar PDP.
Mustapha Sule Lamido ya samu gagarumar nasara a zaben fidda gwanin ya na mai cewa an yi adalci.
Dama an samu rashin jituwa a jam’iyyar a jihar tsakanin tsohon dan takarar jam’iyyar na baya Aminu Ringim da Sule Lamido.
A yanzu dai APC ke mulkin jihar Jigawa duk da gwamnan Badarau Talamiz zai gama wa’adin mulkin sa a 2023.
Jama’ar Aminu Ringim na korafi da nuna son mara baya ga jam’iyyar NNPP ta Rabi’u Musa Kwankwaso.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀