• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DAMUWA DA YANDA A KE SAMUN KARANCIN RUWA A SASSAN NIJAR NA KARUWA

Baya ga bayanai daga yankin Birnin Konni na karancin ruwan sama, yanzu ma an samu irin bayanan a yankin Damagaram.

Damuwar na nuna cewa daidai wannan lokacin na damuna tuni an yi shuka a yankin har shuka ta zauna da yabanya gwanin ban sha’awa.

Daraktan gidan gona na Damagaram Ibrahim Musa ya ce wasu sun yi shuka amma shukar ta bushe.

Musa ya kara da cewa a bara daidai wannan lokacin kauyuka fiye da dubu uku ne su ka yi shuka amma bana sama da 200 ne kacal.

A na sa bangaren shugaban hukumar kula da yanayi Usman Bawa ya ce yanayin iskar da a ke samu na nuna za a samu ruwam ne daki- daki a bana wato ba lokaci daya ba.

Bawa ya ce ba wata damuwa don a karshe za a samu wadataccen ruwan da yardar Allah.

Jami’in ya ce zuwa karshen watan na na Yuli za a samu ruwa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.