• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DAMUNA-HANYA TA YANKE TSAKANIN GADAR MAIWA DA NINGI

Sanadiyyar ruwan sama kamar da bakin kwarya hanyar Gadar Maiwa zuwa Ningi ta yanke inda ya zama ba a iya ketarawa ta bangarorin biyu.

Hanyar dai na da muhimmanci don jama’a da ke bi daga jihohin arewa masu gabar zuwa Kano.

Rahotanni sun baiyana an samu nasarar ceto wasu da su ka fada ruwan da ya yanke Titin ya na wucewa tamkar kogi.

Wani mazaunin Ningi mai suna Auwal Karfe ya ce ya na da uzuri a Bauchi amma ba zai iya wucewa ta hanyar ba sai dai in zai yi zagaye ta Darazo.

Jama’a na yada batun hanyar ta yanar gizo don jan hankalin hukumomi su kawo dauki don gyara hanyar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *