• Thu. Aug 18th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DAMFARA-AN YANKEWA WANI DAN NAJERIIYA DAURIN SHEKARA 7 A AMURKA

ByNoblen

Dec 17, 2021 ,

Bayan cafke dan Najeriya Invictus Obi a Amurka a 2019 da tuhumar damfarar yanar gizo, karshe an yanke ma sa hukunci inda zai zauna a gidan yari har sai shekara ta 2028.
Invictus Obi wanda asalin sunan sa Obinwanne Okeke ne ya dade ya na damfara ta yanar gizo inda ya yi nasarar tara dala miliyan 11.
Okeke ya ce shi dan kasuwar fetur da iskar gas ne kuma ya yi karatu mai zurfi, ya zo ya buge da damfara ta hanyar cutar wasu kamfanoni.
Tun farkon cafke shi ya musanta laifuka biyu da a ke tuhumar sa, inda da ya ga haza sai ya amince da daya daga laifukan a bara don haka a ka soke daya tuhumar.
Okeke zai zauna a gidan yari a garin Oakdale da ke yankin Lousinia ta yamma.
 

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “DAMFARA-AN YANKEWA WANI DAN NAJERIIYA DAURIN SHEKARA 7 A AMURKA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.