• Sun. Dec 5th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DALILIN SAUKE MINISTOCI BIYU DA SHUGABA BUHARI YAYI

ByYusuf Yau

Sep 2, 2021

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi karamin garambawul a gwamnatin sa inda ya sallami ministoci biyu daga aiki.

Ministocin sun hada da na ma’aikatar lantarki Injiniya Saleh Mamman da na aikin gona Sabo Na nono.

Dalilan sauke su ba sa rasa nasaba da rashin tabuka abun kirki.

Tuni shugaban ya sauyawa ministan muhalli Mahmud Muhammad wajen aiki zuwa ma’aikatar gona inda ya tura karamin aiyuka da gidaje Abubakar D Aliyu ya zama ministan wutar lantarki.

Za a jira a ga wadanda za a zabo daga jihar Kano da Taraba don maye gurbin wadanda a ka sauke.

Gwamnatin Buhari ba ta taba sauye-sauye irin wannan ba tun da ta hau gado a 2015.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *