• Sun. Nov 28th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DALILIN DA YASA MUKA YI JUYIN MULKI – SOJOJIN GUINEA

Sojojin kasar Guinea sun ce sun kifar da gwamnatin shugaba Alpha Conde ne don tsanantar cin hanci, keta ‘yancin mutane da barnata tattalin arziki.

Sojojin dai sun kifar da gwmantin Conde bayan barin wuta a wajen fadar shugaban kasar a birnin Conakry.

Kanar Mamadi Doumboya mai shekaru 41 wanda ya jagoranci juyin mulkin ya ce ba su da zabi ne face dawowa da mutane hakkin su.

Doumboya wanda ya dauko kalaman tsohon shugaban Ghna Jerry Rawlings da ya kifar da gwamnati har sau biyu; ya ce matukar a na take hakkin mutane, to ya rataya kan sojoji su kwatowa mutane hakkin su.

Sojojin sun bukaci kowa ya mika wuya don za su sauya gwamnoni da kwamandojin soja.

Hakanan a matakan akwai rufe kan iyakar kasar na mako daya don samun aiwatar da manufar su ta juyin mulki.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “DALILIN DA YASA MUKA YI JUYIN MULKI – SOJOJIN GUINEA”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *