• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DALIBIN KWALEJIN KIMIYYA DA FASAHAR LAFIYA TA AMINU DABO (AD-COHST) YA ZAMA GWARZO A FADIN NAJERIYA.

Dalibin me suna Aliyu Abubakar Dan asalin jahar kano, ya fito ne daga kwalejin kimiyya da fasahar lafiya ta Aminu Dabo dake birnin kano (AD-COHST) a sashen kimiyyar ido.

Kamar yadda shugabar hukumar kula da daliaban kimiyyar Ido ta kasa ta bayyana Farfesa Mrs. Ebele B. Uzodike, tace dalibin ya zama gwarzo ne a wannan sashe a duk fadin kasar ta hanyar jajircewa da kwazo, ta inda yafi kowanni dalibbi daga sassan kasar nan samun maki mafi daraja tare da samun koyarwa daga kwararrun malamai daga makarantar daya fito. Ta bayyana hakanne a ranar bikin yayewa da kuma rantsar da daliban aji na 2018/2019 a sashen kimiyyar ido na makarantun lafiya da jami’o’i a fadin kasar nan ta hanyar kimiyyar yanar gizo Wato zoom, domin kiyaye yaduwar cutar korona a tsakanin al’umma. A jawabinta Mrs.Ebele, ta taya dalibin da kwalejinda ya fito murnar samun wannan nasara, ta kuma hori sauran daliban baya da suyi koyi da shi domin samun sakamako irin nasa. Ta kuma taya dalibai yan uwan kammalawar gwarzon murna tare da horonsu da zama jakadu na gari domin ci gaban al’umma.

Ana nashi jawabin shugaban kwalejin, Akitet Aminu Abubakar Dabo, godewa Allah yayi da samun wannan nasara. A cewarsa wannan nasara ba ta Aliyu ko makarantar kawai bace, sedai nasara ce ga jihar Kano dama kasa baki daya. Dabo ya taya daukacin daluban murna a yayinda ya mikawa gwarzon takaddar shaidar zama gwarzo a kimiyyar lafiyar Ido a kasa baki daya.

Shima gwarzon, Aliyu Abubakar godewa Allah yayi da wannan nasara, sannan ya nuna farin cikinsa a fili tare da haska bukatarsa ta ci gaba da karatunsa a wannan bangare domin habaka lafiyar al’umma a fadin kasar. Aliyu yace yana maraba da kowacce irin dama da gwabnati zata ara mishi na samun tallafin karatu (scholarship) domin daurawa daga inda ya tsaya.

Taron Wanda aka gudanar da shi a babban dakin taro na kwalejin ya sami halartar manyan mutane daga bangarorin kasar nan, a yayinda aka haska hedikwatar da sukeda hakkin yaye daliban ta kimiyyar taro na zoom a bango domin kowa ya tabbatar ya kuma shaida, anyi zaman ne kowa sanye da takunkumi sannan kuma da tazara duk domin kiyaye lafiyar al’umma.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
44 thoughts on “DALIBIN KWALEJIN KIMIYYA DA FASAHAR LAFIYA TA AMINU DABO (AD-COHST) YA ZAMA GWARZO A FADIN NAJERIYA.”

Leave a Reply

Your email address will not be published.