• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DALIBAI DA MALAMAN KOLEJIN NUHU BAMALLI SUN KUBUTA DAGA BARAYI

Dalibai 6 da malamai biyu na kolejin Nuhu Bamalli da ke Zaria sun kubuta daga hannun barayi wata daya bayan sace su.

Jaridar yanar gizo ta Premium Times ta ruwaito cewa an sako wadanda a ka sace bayan iyaye ko dangin su sun biya barayin kudin fansa.

Rahoton ya ce an sako mutanen a kauyen Sabon Birni da ke kusa da Kaduna.

Ba a samu labarin jimillar kudin fansar da a ka biya ba.

Har yanzu gwamnatin jihar Kaduna na kan ra’ayin ba biyan kudin fansa don yin hakan zai karawa barayi karfi ne.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *