• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DALA NA NEMAN KAUCEWA MATAKAN SAUKO DA ITA A KASUWAR CANJI

Dalar Amurka na kaucewa kusan duk matakan da hukumomi ke dauka don rage farashin ta a kasuwar canji dama kasuwar hukuma.

A canjin banki dalar ta kara haurawa fiye da Naira 430 da hakan ke nuna lamarin ya taba dukkan sassan hada-hadar dalar.

A kasuwar canji dai dalar ta cilla zuwa Naira 680 duk da saukowa da ta yi zuwa N660 bayan matakin rage farashin ta da a ka yi.

Shugabannin ‘yan kasuwar canjin a Abuja sun amsa kiran hukumar yaki da cin hanci EFCC na taimakawa don sauko da farashin dalar inda su ka yi yekuwar a dawo da ita Naira 630 amma da alamu har yanzu tsarin bai shiga jikin ‘yan kasuwar ba.

Tashin farashin dala har kullum na zama ginshikin dalilan tashin farashin kayan masarufi.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.