• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DALA NA KARA TSADA A KASUWAR CANJI A NAJERIYA

Yanzu haka takardar kudin Amurka wato dala na kara tsada a kasuwar canjin Najeriya inda ta doshi naira 500 kan dala daya.

Wannan hakika ya shafi farashin muhimman kayan masarufi da kawo tsadar rayuwa.

Wasu matakan babban bankin Najeriya da ke nasaba da samun kudin ketare na daga dalilan kara faduwar darajar Naira.

Su kuma masu sarar kaya a ksn iyakar Najeriya da Nijar na nuna farin ciki kan yanda Naira ta samu koma baya don hakan ya kawo rangwamen farashin kaya.

Takardar Saifa da kasashe rainon Farasnshi da ke makwabtaka da Najeriya ke amfani da ita ta fi Naira daraja don haka ma’abota kan samu saukin farashin hajar su ke oda daga Najeria zuwa Nijar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
34 thoughts on “DALA NA KARA TSADA A KASUWAR CANJI A NAJERIYA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.