Matakin da gwamnatin Najeriya ta dauka na dakatar da aikin dandalin sadarwa na twitter ya haddasa yabo da suka ga gwamnatin.
Masu ganin matakin zai taimaka wajen rage kaifin kamfen din wargaza Najeriya na mara baya da nuna hakan ya yi daidai kuma alherin hakan ya fi asarsr yawa.
Sai kuma a gefe guda masu wuni su na aika sakonni ta twitter da masu marawa ‘yan Biafra baya na jin taksicin mstakin da rubuta sakonnin caccakar gwamnati har ma da nuna hakan tauye ‘yancin furta ra’ayin ‘yan kasa ne.
Irin wannan mataki ba sabam ba ne ga gwamnatin Buhari da ba ta daukar matakan dirar mikiya kamar yanda a ka yi tsammani za ta yi lokacin da ta hau mulki a 2015.
Ministan labaru Lai Muhammed ya kuma kara da umurnin fara rejistar kamfanonin sadarwar yanar gizo da yiwuwar daukar mataki a kan su in sun sabawa doka.