• Sun. Nov 28th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DAKATAR DA TWITTER-GWAMNATIN NAJERIYA BA TA TAUYE ‘YANCIN FADAR RA’AYI BA

Gwamnatin Najeriya ta ce sam ba ta tauyewa kowa ‘yancin fadar ra’ayi ba sakamakon dakatar da aikin twitter.

Wannan bude kariya ce ta gwamnatin a gaban kotun Ecowas a Abuja biyo bayan karar da wata kungiya ta kai gwamnatin ta na son kotu ta dakatar da matakin na gwamnatin Najeriya da nuna hakan take hakkin fadar ra’ayi ne.

Gwamnatin ta ce akwai bambanci tsakanin ‘yancin ra’ayi da kuma dakatar da aikin wanu kamfanin kasuwanci na Amurka a Najeriya don saba dokokin Najeriya.

Gwamnatin ta kara da cewa a bisa doka kamfanin twitter na ‘yan kasuwa ba ya karkashin kariyar wata doka ta kasa da kasa da har dakatar da aikin sa zai zama fassarar hana wani ‘yanci.

Kotun dai ta dakatar da gwamnatin Najeriya daga hukunta masu aiki da twutter ta barauniyar hanya har sai ta kammala sauraron karar da kungiyar ta SERAP da wasu mutum 176 su ka shigar ta hannun babban lauya Femi Falana.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *