• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DAKARUN YAMAM SUN KARFAFA TSARO A FAFATAWAR DA SU KE YI DA ‘YAN HOUTHI KAN MARIB

ByNoblen

Nov 18, 2021

Dakarun gwamnatin Yaman sun karfafa tsaro a yakin da su ke yi da ‘yan tawayen houthi a yankin Marib.
Shi dai yankin mai arzikin iskar gas, ya kasance shi kadai ne mai tasiri a hannun gwamnatin ta birnin Aden a arewacin kasar da ‘yan tawayen su ka ragargaza.
Ministan labarun kasar Mu’ammar Al-Eryani ya ce an tura daruruwan dakaru don karfafawa sojojin da ke bakin daga da rundunar larabawa da Saudiyya ke jagoranta wajen tunkarar barazanar ta houthi.
‘Yan tawayen na houthi da Iran ke daukar nauyi sun hana gwamnatin Abed Rabbo sakat tun 2014 inda su ka rike da babban birnin kasar Sanaa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.