• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DAGA FARKON WATAN NAN NA AGUSTA BAKI MASU RIGAKAFI ZA SU IYA SHIGA SAUDIYYA

ByNoblen

Jul 31, 2021 , ,

Daga farkon watan nan na Agusta baki da su ka samu rigakafin korona bairos za su iya shiga Saudiyya ba tare da bukatar killacewar kwana 14 ba.

Ministan yawon bude ido na kasar Ahmed Alkhatib ya baiyana haka.

Matukar mai son ziyara ya samu yin rigakafi na farko da na biyu zai iya shiga Saudiyya rike da takardar shaidar rigakafin.

Kasar ta amince da rigakafin AstraZeneca, Pfizer da Moderna.

Alkhatib ya ce Saudiyya na maraba da karbar baki bayan dakatarwa ko takaita hakan sanadiyyar annobar korona.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *