• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DABARUN ‘YAN TAKARAR SHUGABANCIN NAJERIYA

‘Yan takarar shugabancin Najeriya na bin dabarun samun hadin kan wakilai da za su zabi dan takara don tsarin daidatawa wajen fidda gwani ya samu tangarda don tasirin masu takarar.

Wannan na zuwa ne gabanin tarukan fidda gwani na jam’iyyu a karshen watan nan don mika sunaye ga hukumar zabe a ranar 3 ga watan gobe.

Kusan dukkan ‘yan takarar na manyan jam’iyyu na da ra’ayin shata daga a taron fidda gwani inda kuri’ar wakilai za ta raba gardama.

Hakan na daga dalilan ziyarce-ziyarcen ‘yan takarar jihohi don neman goyon baya da fahimtar wadanda a ke tare da inda a ke da kalubale.

Sabon dan takarar shugaban kasa a PDP tsohon jami’in banki Muhammad Hayatudeen ya ce ba ya shakkar zaben fidda gwani a jam’iyyar sa da y a ce ya na da kwarin guiwar za ta lashe zabe in masu ruwa da tsakin ta su ka hada kai.

Haka shi ma gwamna Bala ,Muhammad da ke cikin ‘yan takarar ke cewa sai da ya yi tuntuba mai zurfi kafin aiyana tsayawa.

A APC mai gwamnatin taraiya uban jam’iyyar Bola Tinubu na shirin haduwa da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo don neman goyon bayan wakilai musamman na kudu maso yamma. Wannan na zuwa yayin da gwamna Fayemi na Ekiti ya shigo jerin ‘yan takarar inda tsohon gwamnan Ogun Ibikunle Amosun ke kimtsawa.

Hakika gwamnoni na da tasiri ga zaben fidda gwani da hakan ya sa na tambayi gwamna Muhammad Inuwa Yahaya me zai ce kan hakan.

Gwamnan ya ce ya yarda su na da tasiri kamar yanda sauran ‘yan jam’iyya su ke da tasiri amma akwai dan takarar da ya je jihar sa bai kai ma sa ziyara ba.

Za a jira a ga yanda duk ‘yan takarar za su kai matakin karshe ne na fidda gwani ko wasu za su janyewa wasu.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.