• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DA NETANYAHU DA BENNET DUK SAMMAKAL-PALASDINAWA

Palasdinawa na nuna ba wani bambanci da za a samu ga wanda hadakar jigogin siyasa a Israila za su nada ya amshe madafun iko daga firaminista Benjamin Netanyahu wato Naftali Bennett.

Majalisar dokokin Israila Knesset za ta amince Nattali Bennet ya zama sabon furaminista inda bayan shekaru biyu Yeir Lapid zai karbe shi ya karisa wa’adi.

Hadin guiwar zai kawo karshen dogon mulkin Benjamin Netanyahu da zargin cin hanci da rashawa ya yi ma sa illa ainun.

Palasdinawa na cewa ba sa ganin samun wani canji don kawar da Netanyahu bisa dalilin shi kan sa Bennett ya zauna a yankunan da Israila ta mamaye da karfin soja a yankunan na Palasdinawa.

Kazalika Palasdinawa na cewa Bennett zai dage watakil ya wuce Netanyahu tsaurin ra’ayi don samu  karbuwa daga muguntar Yahudawa.

Kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas ta ce duk shugabannin Israila a wajen ta Danjuma ne da Danjummai.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “DA NETANYAHU DA BENNET DUK SAMMAKAL-PALASDINAWA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.