• Tue. Nov 30th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DA JAKUNA MU KE HUDA DON A KAN KWACE MA NA SHANU-MUHAMMAD DAURAN ZURMI

Wani mazaunin yankin Dan-dauran a karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara Muhammad  Dandauran, ya ce kalubalen tsaro ya sa da jakuna ko babura su kan daurawa garma wajen huda a gonakin su.

Muhammad Dan-dauran a zantawar sa da Muryar Amurka, ya ce kalubalen barayi da kan fake a dajin Zurmi ke zama mu su cikas wajen noma da kiwon shanu. 

Mutumin karkarar ya ce matukar barayin su ka samu mutum a gona da shanu, za su kwace shanun don haka su kan yi amfani da hanyoyi na daban wajen huda.

Hakanan Dandauran ya ce barayin kan yi wa kauyen kofar rago su shiga har cikin gidaje su kwashe duk wasu kaya masu daraja in kuma tsautsayi ya ratsa a samu asarar rai.

Rahotanni na nuna yanzu an tura sojoji don kare yankin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *