• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DA ALAMUN ‘YAN KAMFEN DIN PDP SUN FARA GAJIYA DA CACCAKAR WIKE

ByNoblen

Sep 12, 2022

Alamu na nuna kamfen din dan takarar shugaban kasa na babbar jam’iyyar adawar Najeriya PDP ya fara gajiya da zafin caccakar da gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike ke yi wa tafiyar.

An gano gajiya da hakan ne tun taron da manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar su ka yi da mara baya ga shugabancin Iyorchia Ayu wanda Wike y adage kai da fata sai ya yi murabus don mukamin ya koma yankin kudu.

Dabarar saukar shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar Walid Jibrin daga arewa da ya dora mataimakin sa Adolphus Wabara a kujerar daga kudu bai gamsar da Wike da magoya bayan sa ba.

Gwamnan Binuwai Samuel Otom ne kadai gwamnan PDP daga arewa da ke marawa Wwike baya 100% da hakan ke zagon kasa ga kamfen din Atiku Abubakar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “DA ALAMUN ‘YAN KAMFEN DIN PDP SUN FARA GAJIYA DA CACCAKAR WIKE”

Leave a Reply

Your email address will not be published.