• Wed. May 25th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DA ALAMUN SAMUN MIKA WUYA DAGA UKRAIN-MINISTAN WAJEN RASHA SERGEI LAVROV

Ministan wajen Rasha Sergei Lavrov ya ce da alamun mika daga bangaren Ukraine a tattaunawar da a ke yi ta samun matsaya kan mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine din.
Lavrov ya ce ya ga kwarin guiwar samun cimma matsaya daga bangaren hukumomin Kyiv.
Lavrov ya ce sassautowar matsayar siyasa da ta sojan Ukraine don samun kariyar tsaro daga Rasha na daga muhimman lamuran da a ke tattaunawa a kai.
Shugaban Ukraine Vlodymyr Zelenskyy ya ce ya zama sai dai kasar sa ta amince ba za ta zama memba a kungiyar tsaron yammacin turai wato NATO ba.
Dama cikin manyan dalilan da Rasha ta yi dogaro da su wajen aukawa mamaye Ukraine kawai batun shigar Ukraine din NATO.
An ruwaito Zelenskyy na cewa a shekaru da dama an samu hasken kofar Ukraine ta zama memba a NATO amma yanzu kuma kama kofar yin hakan ta rufe.
In za a tuna Ukraine ta bukaci NATO ta dau matakin hana jirage tashi a yankin Ukraine da hakan zai sa harbor duk wani jirgin Rasha da ke shawagi.
Nato ta nun aba zai yiwu ta dau matakin ba don yin hakan zai kara fadada yaki ne da zai shafi kasashen turai.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
5 thoughts on “DA ALAMUN SAMUN MIKA WUYA DAGA UKRAIN-MINISTAN WAJEN RASHA SERGEI LAVROV”
  1. Thank you for another informative website. The place else could I am getting that kind of information written in such a perfect means? I have a undertaking that I am just now running on, and I have been at the glance out for such info.

  2. Hmm is anyone else having problems with the images
    on this blog loading? I’m trying to figure out if its a problem on my end
    or if it’s the blog. Any feed-back would be greatly
    appreciated.

Leave a Reply

Your email address will not be published.