• Thu. May 19th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DA ALAMUN RUWAN SAMA YA FARA KANKAMA A AREWA TA TSAKIYAR NAJERIYA

A karshen mako an tabka ruwa a yankunan babban birnin Najeriya Abuja da jihar Nassarawa inda a ka yi yayyafi a jihar Filato.

Wannan na nuna fara zaman damuna da niyyar komawa gona.

Ruwan ya mamayi matuka mota da ba su da na’urar goge gilashi ko na’urar sanyi da za ta taimaka wajen ganin hanya. Hakan ya sa wasu samun waje su ka tsaya don jiran tsagaitawar ruwan kafin su cigaba da tafiya.

Ruwan ya kwanta kan tituna da hakan ya zama wajibi matafiya su rika takatsantsan don kar a samu cikas.

Lamuran rashin tsaro na barazana ga manoma da gonakin su ke can cikin daji.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.