• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DA ALAMUN BASHIR MACHINA YA SAMU NASARA KAN AHMED LAWAN

ByYusuf Yau

Jun 25, 2022

Matakin da hukumar zaben Najeriya ta dauka na aiyana Bashir Machina a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na majalisar dattawa a inuwar APC a Yobe tsakiya ya sanya shi alamun galabar kan shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan.

In za a tuna Lawan wanda ya nemi tikitin takarar shugaban kasa a APC amma bai samu nasara ba, ya dawo don karbar takarar majalisar dattawa amma ya samu cikas daga wanda ya lashe kujerar.

Hukumar zaben dai ba ta ambaci sunan Ahmed Lawan ba amma ta aiyana Machina a matsayin wanda ta sani a matsayin dan takara.

Jam’iyyar APC karkashin Abdullahi Aadamu na marawa Ahmed Lawan baya ne don haka har gargadi Adamu ya yi wa Mahina na ya yi takatsantsan.

Za a jira a ga yanda wannan dambarwa za ta kammala inda gabanin nan ma Machina ya nufi kotu don kalubalantar tura sunan Lawan don takarar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “DA ALAMUN BASHIR MACHINA YA SAMU NASARA KAN AHMED LAWAN”

Leave a Reply

Your email address will not be published.