• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DA ALAMU ZA A KAI RUWA RANA TSAKANIN ‘YAN MAJALISA KAN TWITTER

Alamu na nuna za a iya samun kai ruwa rana a majalsar dokokin Najeriya tsakanin ‘yan majalisar kan dakatar da aikin tiwita da shugaba Buhari ya amince da yi.

Tuni a bayan fage wasu ‘yan majalisar su ka ka fara nuna aniyar su ta gabatar da ra’ayi kan lamarin gaban majalisar s talatar nan.

Kuma manuniya na nuna muhawarar za ta faru ne tsakanin akasarin ‘yan APC masu mara baya ga matakin da ‘yan PDP masu adawa.

Kazalika muhawarar ka iya zafi tsakanin ‘yan arewa masu mara baya ga dorewar dunkulalliyar Najeriya da kudu masu gabar da ‘yan majalisar su ke shan matsin lamba daga ‘yan awaren Biafra na furta kalamai masu zafi da za su zafafa siyasar Najeriya.

Muhawarar ta danganta ga yanda shugabannin majalisa za su yanke matsayar ba da damar tattaunawar ko taka ma ta birki don kaucewa rudani.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
43 thoughts on “DA ALAMU ZA A KAI RUWA RANA TSAKANIN ‘YAN MAJALISA KAN TWITTER”

Leave a Reply

Your email address will not be published.