• Thu. Dec 9th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DA ALAMU ZA A DAWO DA IGBOHO NAJERIYA DAGA KOTONO

Da alamu gwamnatin jamhuriyar Benin za ta iza keyar dan bangar yarbawa Sunday Igboho zuwa Najeriya bayan cafke shi ranar litinin.

Igboho wanda ya sulale daga Najeriya bayan yunkurin zanga-zangar kafa kasar yarbawa,  ya shiga Benin da nufin arcewa zuwa Jamus sai ‘yan sanda su ka kama shi a filin jirgin saman Kotono.

Igboho wanda ke son a kori dukkan Fulani daga jihohin yarbawa, ya yi sanadiyyar fitinar da ta kawo asarar rayuka.
Tsarin Igboho tamkar Nmamdi Kanu ne a wajen kabilar Igbo.

Zuwa yanzu gwamnatin Najeriya ba ta yi martani kan cafke Igboho ba.
Tuni wasu kungiyoyin kare muradun yarbawa ke adawa da neman dawo da Igboho Najeriya da nuna ba za a yi ma sa adalci ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *