• Thu. May 19th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DA ALAMU WUTA TA DAWO A NAJERIYA BAYAN BACIN DA TUSHEN WUTAR YA YI

ByYusuf Yau

Apr 10, 2022

Da alamu an shawo kan daukewar wuta a Najeriya bayan bacin da layin wutar na taraiya ya yi.
An dauke wutar a yammacin jumma’a inda zuwa dare kasa ta dau duhu sai inda a ke da na’urorin samar da wuta na janareta ko hasken rana.
Wannan daukewar wuta na ‘yar gaba na neman zama jiki don a ‘yan kwanakin baya ma an samu hakan.
Daukewar wutar lantarki a wasu sassan ya fi samun wutar yawa.
Rashin wadatar lantarki ko sayar da ita kan farashi mai ragusa na zama babban kalubale ga talakawa musamman masu kananan sana’o’i da ke aiki da wuta.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI๐Ÿ˜€๐Ÿ˜€๐Ÿ˜€
4 thoughts on “DA ALAMU WUTA TA DAWO A NAJERIYA BAYAN BACIN DA TUSHEN WUTAR YA YI”
  1. Hello everyone, it’s my first pay a quick visit at this website,
    and article is really fruitful in support of me,
    keep up posting these content.

Leave a Reply

Your email address will not be published.