• Tue. Nov 30th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DA ALAMU RASHIN SAMUN NASARAR AKASARIN JAMA’A SU HADA LAYUKA DA NIN YA SA KARA WA’ADI

Alamu na nuna rashin samun akasarin jama’ar da ke amfani da salula a Najeriya su hada layukan su da shaidar dan kasa “NIN” ya sa kara wa’adin ranar rufe rejistar.

Hukumar sadarwa ta baiyana sabuwar ranar zuwa 26 ga watan nan na Yuli.

Yanzu ba a samun wani cikas wajen samun shaidar zama dan kasa don yanda a ka bude cibiyoyi masu zaman kan su na gudanar da rejistar a madadin gwamnati.

Wani abun la’akari shi ne yanda wasu kan karbi shaidar amma sai su yi kasa a guiwa wajen hada layukan na su don shagulgulan rayuwar yau da kullum.

Zai yi wuya wanda bai yi rejistar ba ko ma wanda ya yi ya wuni ya na buga waya ba tare da ya samu sakon tunatarwa kan yin rejistar ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *