• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DA ALAMU KWAMITIN SULHU NA ATIKU DA WIKE ZAI FARA AIKI YAU DIN NAN

Alamu na nuna a litinin din nan kwamitin da dan takarar PDP ga zaben 2023 Atiku Abubakar da gwamnan Ribas Nyesom Wike zai fara aikin sulhu.

An kafa kwamitin a makwan jiya a wani taro da bangarorin biyu su ka gudanar a gidan tsohon ministan labaru Jerry Gana.

Kwamitin dai na mutum 14 zai zauna don duba yanda zai sulhunta rashin jituwa daga bangaren Wike tun bayan rashin daukar sa a matsayin mataimaki da Atiku ya yi.

In za a tuna Atiku ya dau gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakin sa a takarar da a ke ganin za su fi jituwa in an kwantan ta irin dabi’un Wike na fito na fito.

Za a jira a ga yanda sulhun zai tafi yayin da Wike ke kara mu’amala da ‘yan jama’iyyar APC har ma da gaiyatar su don buda wasu aiyuka da ya gudanar a jihar sa ta Ribas.

Cikin manyan ‘yan APC da su ka shiga RIbas bisa gaiyatar Wike akwai Sanata Magatakarda Wamakko da kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.