• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

DA ALAMU ABDULJABBAR NA NEMAN WARWARE TUBAR DA YA YI

Da alamu Abduljabbar Kabara na yunkurin janye tuba ko ba da hakuri da ya yi bisa kalaman batance ga manzon Allah da sahabban sa.

Kwana biyu bayan yada kalaman neman ahuwar sa, an sake jin wani faifai da ya ke zaiyana mulabalar da a ka yi da shi a matsayin wasan kwaikwayo.

Abduljabbar ya ce sai da a ka shirya abubuwan da a ka kunna ma sa a wajen mukabalar kafin a zauna da shi.
Alamu na nuna kamar Abduljabbar wanda ya kasa ba da amsar ko daya daga tambayoyin da a ka yi ma sa, na son dawo da kaifin bayanan sa a zukatan magoya bayan sa da jikin su ya yi sanyi daga yanda mukabalar ta kasance ba hujja ko daya.

Yanzu dai a na jiran gwamnatin jihar Kano ta fito da amtakin da za ta dauka kan Abduljabbar bayan faduwa kasa warwas a mukabala.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2,778 thoughts on “DA ALAMU ABDULJABBAR NA NEMAN WARWARE TUBAR DA YA YI”