• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

CIRE TALLAFIN FETUR MU KA YI BA KARA FARASHIN FETUR BA – INJI SHUGABAN NNPC MELE KYARI KOLO

Shugaban  kamfanin man fetur na Najeriya Mele Kyari Kolo ya ce ba kamar yanda ake ambata cewa gwamnati ta karawa litar man fetur farashi ba, gaskiyar maganar gwamnati ta janye tallafin da ta ke bayarwa ne ba wai farashi ta kara ba. Mele Kolo da ke zantawa da manema labaru, ya ce illar da gwamnati ta lura ba da tallafin man fetur na jawowa tsawon shekaru ya sanya gwamnatin cire tallafin gaba daya. Kolo ya kara da cewa wasu mutane kalilan ne watakil har da shi kan sa, ke cin gajiyar tallafin, inda talakawa basa amfana.

Shugaban na NNPC ya ce gaskiya ne talakawa kan samu saukin fetur in akwai tallafi, amma yanzu Najeriya da ma sauran kasashen duniya na cikin yanayi tabarbarewar tattalin arziki da irin ba da tallafin ba zai cigaba da dorewa ba. Hakanan tallafin kan jawo ‘yan kasuwa su yi ta korafin su na bin gwamnati bashin da ba ta biya su har ya kai ga samun dogayen layukan man fetur.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “CIRE TALLAFIN FETUR MU KA YI BA KARA FARASHIN FETUR BA – INJI SHUGABAN NNPC MELE KYARI KOLO”
  1. Do you mind if I quote a couple of your posts as long as I provide credit and sources back to your site?
    My blog site is in the very same area of interest as
    yours and my users would definitely benefit from some of the information you
    present here. Please let me know if this ok with you. Thank
    you!

Leave a Reply

Your email address will not be published.