• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

CIN GASHIN KAI-LAUYOYI SUN YI ZANGA-ZANGAR MARA BAYA GA MA’AIKATAN SHARI’A

Kungiyar lauyoyin Najeriya ta gudanar da zanga-zangar mara baya ga kungiyar ma’aikatan shari’a da ke yajin aikin neman cin gashin kai.

Lauyoyin sun yi dafifi a majalisar dokokin Najeriya da nufin shiga don zaiyana korafin sashen shari’a amma jami’an tsaro sun rufe kofofi biyu na majalisar kirib.

Rahoto na nuna cewa akwai fargabar jami’an sashen zartarwa ta barin sashen shari’a ya samu ‘yanci don hakan barazana ce ga ‘yan siyasa da za su iya hukunta su cikin sauki in sun aikata laifi.

Tun 6 ga watan nan na Afrilu ma’aikatan shari’ar ke yajin aiki da hakan ya kassara zaman kotuna.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *