• Wed. Dec 1st, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

CIGABA DA YAJIN AIKIN ALKALAI NA KAWO CIKAS GA WADANDA KE YARI-MASU SHARHI

Tsawon yajin aikin ma’aikatan sashen shari’a a Najeriya ya kawo koma bays ga lamuran adalci don yanda rashin zaman kotuna ya bar wadanda a ke tuhuma da dama a gudajen yari ko ofisoshin ‘yan sanda.

Tun fara yajin aikin ma’aikatan a farkon watan Afrilu, a ke tattaunawa da sashen zartarwa amma ba a samu bakin zare ba.

Tasirin yakin aikin ga tafiyar da lamura na kasa baki daya ya sa babban alkali Jostis Muhammad Tanko kira ga ma’aikatan su dawo aiki duk da baya son sa baki ga lamuran gwamnoni don kada hakan ya zama neman alfarma daga sashen shari’a da tambarin sa shi ne adalci ga kowa.

Ma’aikatan sashen shari’ar sun shiga yajin aikin don tilasta gwamnatin taraiya da gwamnoni su bi hukuncin kotu na samun ‘yancin gashin kan kudin sashen shari’a.

Kwamishinan shari’a na jihar Gombe Barista Zubairu Ciroma na fatar samun sulhu don yanda rashin zaman kotunan ke take ‘yancin masu bin shari’a.

Hakanan shi ma dattijon Nepu Sawaba Alhaji Hussaini Gariko ya bukaci gwamnati ta duba kadun alkalan don jinkirta adalci nau’i na zalunci.

Yajin aikin ya sanya lauyoyi yin zanga-zanga zuwa majalisar dokokin Najeriya don neman su sa baki wajen tilastawa sashen zartarwa ya sakewa shari’a mara; inda da alamu sashen zartarwa ba ya sha’awar sakewa alkalai ‘yanci 100% don gudun fadawa tsaka mai wuya ba tare da da damar rike linzami ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *