• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

CIBIYAR ‘YANCIN DAN ADAM TA MAJALISAR DINKIN DUNIYA ZA TA BINCIKA RUWAN WUTA KAN GAZA

ByNoblen

May 29, 2021 , , ,

Cibiyar kare ‘yancin  dan adam ta majalisar dinkin duniya za ta shiga binciken murgunawa jama’a da Isra’ila ta yi a ruwan wuta da ta yi kan Gaza na tsawon kwana 11. Binciken zai shafi laifukan da a ka yi a yankin Isra’ila.

Ruwan wutan Isra’ila ya yi sanadiyyar kashe Palasdinawa 253 ciki kuma da yara 66 da raunata fiye da mutum dubu 1,900.

Gudanar da binciken ya samu nasara ce bayan kasar Pakistan ta gabatar da kudurin inda da kyar a ka samu rinjaye da kasa daya wato an samu kasashe 24 sun amince cikin 47 kan a gudanar da binciken don bankado jibgin laifukan da a ka aikata na yaki.

A jawabin budewa jagorar ‘yancin dan adam ta majalisar Michelle Bachelet ta nuna damuwa kan yawan mutanen da a ka kashe a Gaza da nuna hakan zai jawo samun aikata laifin take ka’idojin yaki.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
4 thoughts on “CIBIYAR ‘YANCIN DAN ADAM TA MAJALISAR DINKIN DUNIYA ZA TA BINCIKA RUWAN WUTA KAN GAZA”
  1. Having read this I thought it was very informative. I appreciate you spending some time and energy to put this information together. I once again find myself spending a lot of time both reading and leaving comments. But so what, it was still worthwhile!

Leave a Reply

Your email address will not be published.